Oman ta karbi wasu fursunonin Amurka shida

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Amurka na shirin rufe Guantanamo Bay

Amurka tace ta kwashe wasu fursunoni 'yan Yemen su shida da ake rike da su shekara da shekaru daga wajen tsare mutane na Guantanamo Bay zuwa kasar Oman.

Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon tace tana godiya ga kasar ta yankin Gulf game da abinda ta bayyana da jinkan data nuna

Ta kuma godewa Kasar Oman saboda shirinda ta yi na goyawa Amurka baya a kokarin da take na rufe sansanin na Guantanamo.

Shugaba Obama ya yi alkawarin rufe sansanin ne a lokacin yakin neman zabarsa a shekarar 2008, amma bai iya cika alkawarin nasa ba.

Gwamnatinsa ta rage yawan fursunonin dake gidan yarin zuwa rabi