Shugaba Al-Bashir ya bar baya da kura

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana sa rai al-Bashir zai yi wa manema labarai jawabi da zarar ya isa Khartoum.

Shugaba Omar al-Bashir na Sudan ya fice daga Afirka ta Kudu duk da umarnin da wata kotu ta bayar na hana shi fita daga kasar.

Kotun dai, wacce ke birnin Johannesburg, ta bayar da umarnin ne har sai ya amsa zargin da kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta yi masa kan laifukan yaki, ICC.

Al-Bashir ya je kasar ne domin halartar taron da shugabanin kungiyar kasashen Afirka ke yi a kasar.

Wakiliyar BBC ta ce ana sa ran al-Bashir zai yi wa manema labarai jawabi kan batun da zarar ya sauka a Khartoum, babban birnin kasar.

Kotun ICC na son a gurfanar da al-Bashir a gabanta domin ya amsa zarge-zargen da ake yi masa kan iza rikicin da aka yi a yankin Darfur a shekarun baya.

A ranar Litinin ne wata kotu a Afirka ta Kudu za ta yanke hukunci a kan ko kasar za ta mika Al-Bashir ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka, ICC.