Boko Haram: Amurka za ta ba da $5m

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Barrack Obama

Gwamnatin Amurka ta ce za ta bayar da $5m ga rundunar hadin gwiwa ta kasashen da ke makwabtaka da Tafkin Chadi domin yaki da Boko Haram.

Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da nahiyar Afirka, Linda Thomas-Greenfield ce ta bayyana hakan a wata tattaunawa da ta yi da manema labarai ta waya daga Afirka ta Kudu.

Ta ce hukumomin Amurka ba sa daukar matsalar Boko Haram a matsayin matsalar Najeriya ita kadai, shi ya sa kasar take aiki da Najeriya da sauran kasashen yankin don kawo karshen kungiyar.

Mis Thomas-Greenfield ta ce Amurka na duba yiwuwar kara tallafin da take bai wa Najeriya karkashin gwamnatin Muhammadu Buhari.

A makon jiya ne dai shugabannin kasashen yankin Tafkin Chadin suka gudanar da wani taro a Abuja, babban birnin Najeriya, inda suka amince da wasu kudurori guda goma, da suka hada da ajjiye hedikwatar rundunar, a birnin N'Djamaena na Chadi a karkashin jagorancin Najeriya.