An gano gidan sayar da jarirai a Enugu

Hakkin mallakar hoto google
Image caption 'Yan sandan Najeriya

A Najeriya, rundunar 'yan sandan jihar Enugu tana gudanar da bincike game da wani gida da ta bankado, inda ake zargin an ajiye wasu mata 9 masu dauke da juna biyu.

Rahotanni sun ce an girke matan ne inda ake kula dasu da nufin in sun haihu, a sayar da jariran nasu.

Sai dai mutumin dake da gidan da aka gano matan ya ce yana taimaka masu ne, amma rundunar 'yan sandan ta ce tana gudanar da binciken ne domin gano gaskiyar lamarin.

Matan wadanda suka hada da masu shekaru 17 da 19 da 21 da kuma 24 sun ce an musu hanya ne zuwa gidan bayan sun rasa yadda zasu yi da cikin da suka samu batare da aure ba.