CBN ya dakatar da 'yan canji

Babban Bankin Najeriya

Asalin hoton, cbn facebook page

Bayanan hoto,

Babban Bankin Najeriya

Babban bankin Najeriya, CBN ya dakatar da 'yan canji 437 daga samun sayar da dalla na mako-mako a kasuwar hada-hadar kudaden kasashen waje.

Bankin ya hana su damar samun dala dubu 30,000 wadda ake bai wa 'yan canji duk mako.

Kazalika, bankin ya ci tarar 'yan chanjin N2m sakamakon rashin bayar da bayanan yadda suka yi amfani da kudaden kasar waje da bankin ya sayar musu duk wata.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Babban bankin ke dakatar da 'yan chanjin ba.