'An kashe wani jigon Al-Qaeda, Belmokhtar'

Hakkin mallakar hoto a
Image caption Mokhtar Belmokhtar

Jami'ai a Libya sun ce harin bama bamai ta sama da sojojin Amurka suka kai ya halaka wani jigo a kungiyar Al-Qaida da ake nema ruwa a jallo.

Mokhtar Belmokhtar shi ya bada umurnin kaddamar da hari a wata cibiyar tara gas a shekara ta 2013, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar ma'aikata 40 'yan kasashen Amurka da Burtaniya.

Hukumomin sojin Amurka sun ce bama baman da suka harba sun fada inda ake so, sai dai har yanzu basu tabbatar da mutuwar Belmokhtar ba.

Jiragen yakin Amurka sun harba bama baman ne a maboyar Belmokhtar dake gabashin birnin Tobruk, da nufin halaka jigo a kungiyar ta Al-Qaida.

Mokhtar Belmokhtar ya yi fice a matsayin daya daga cikin 'yan ta'adda mafiya hadari a Afirka, kuma har ya taba rasa idon sa daya a wajen gumurzu a Algeria, har yakai ana yi masa lakabi da Mr. Malboro.