An yi jarabawa ta duk kasa a Somalia

Image caption Dalibai na alfahari da wannan jarabawar

A karon farko cikin shekaru 25, dalibai fiye da 7,000 sun yi jarabawa ta duk kasa a yankin tsakiya da kuma kudancin kasar Somalia.

Fannin ilimi shi ne ya fi durkushewa tun bayan da yakin basasa ya barke a kasar a shekarar 1991.

Tun daga lokacin babu gwamnatin tarayya a Somalia a yayinda makarantu suka za bi manhajar karantun da ya fi dacewa da su.

Cikin wadanan shekaru, ana koyar a dalibai cikin harsuna daban-daban.

Wata daliba mai suna Haji Abdullahi ta ce "Wannan jarabar na da bambamci da wacce ta nasaba yi, ina alfaharin kasancewa daya daga cikin daliban da suka soma zama a wannan jarabawar.