Menene ke janyo auren wuri a Nigeria?

Image caption Talauci da al'adu da auren zumunci na daga cikin abubuwan da suke jawo yi wa yara auren wuri

Ana bikin ranar tuna wa da yara a nahiyar Afirka a wani mataki na karfafa gwiwa ga al'umma domin barin yara su cimma burinsu na rayuwa

A shekarar 1991 ce, kungiyar kasashen tarayyar Afirka AU, ta ware ranar 16 ga watan Yunin ko wacce shekara domin tuna wa da daruruwan yara 'yan makaranta da aka kashe a shekarar 1976 a garin Soweto na kasar Afirka ta Kudu.

Taken ranar na wannan shekarar shi ne, hada kai wajen kawo karshen yi wa 'ya'ya mata auren wuri.

Halima Nuruddeen wata jami'a ce a kungiya ce mai fafutukar ganin an ilmantar da 'ya'ya mata a Afirka da ke Najeriya, African Female Youth and Students Development Initiative ta ce, ana samun karuwar yi wa 'yan mata musamman a yankin arewa maso gabashin kasar auren wuri.

Halima ta kara da cewa "talauci da al'adu da auren zumunci na daga cikin abubuwan da suke jawo irin wannan matsaloli."

A jamhuriyar Nijar kuwa rahotanni sun ce ana samun raguwar matsalar cin zarafin mata, inda iyaye suka fara mika wuya wajen barin 'ya'yansu su yi karatun mai zurfi.