An kashe jagoran Al-Qaeda a Yemen

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kisan jagoran Al_Qaeedan a Yemen babban komabaya ne ga kungiyar

Kungiyuar Al Qaeda a Yemen ta tabbatar da cewa an kashe jagoranta Nasir al Wuhayshi yayin wani harin sama da sojojin Amurka suka kadddamar.

Ta sanar da mutuwarsa ne a wani bidiyo da ta saka a shafin Intanet

Tunda farko dai rahotanni sun ambato jami'an tsaron Yemen su na cewa an kashe shi ne a ranar Jumu'ar data gabata a tashar jiragen ruwan kudancin kasar ta Mukalla

A baya Nasir al-Wuhayshin ya taba zama na kurkusa da Marigayi jagoran kungiyar al-Qaedan Osma bn Ladan,

Amurka ce kadai take lulawa sama da jirgi marar matuki a kasar Yemen