An kalubalanci Musulman Biritaniya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Likitoci suna yi wa mara lafiya dashen koda

A yayin da watan azumin Ramadan ke kara karatowa, asibitoci a Biritaniya suna kira ga Musulmai da su rika bayar da gudunmuwar kodarsu da hantarsu ga marasa lafiyan da ke bukatar a yi musu dashe.

Akwai kimanin musulmai miliyan 2.7 a Biritaniya, kuma wadanda suke bukatar a yi musu dashen koda ko hanta daga cikinsu kan dade ba su samu wanda zai sadaukar musu da bangaran da suke bukata ba, ba kamar yadda nan da nan wadanda ba musulmai ba ke samun taimakon.

Hakan na faruwa ne sakamakon rashin masu bayar da taimakon, matsalar da ba ta tsaya a Biritaniya ba kawai, amma a wannan rahoto wakilin BBC John McManus, ya fara bincikensa a wani asibiti a Birmingham, wani birni da ke Biritaniya mai yawan musulmai.

'Rayuwa a Birmingham'

Nazma wata matashiya ce musulma wacce take fama da ciwon koda a Birmingham.

Ana yi wa Nazma karin jini na koda sau uku a kowane mako a asibitin Sarauniya Elizabeth saboda yadda ciwon kodar ya yi kamari.

Tana bukatar a yi mata dashen koda amma babban likitan da yake duba ta, Adnan Sharif ya ce yana tunanin sai ta yi jiran tsawon shekaru hudu kafin hakan ya faru saboda rashin wanda zai taimaka ya ba ta kodar da za ta yi daidai da wacce ake bukata.

Lamarin yana bukatar a samu koda da ta yi daidai da kwayoyin halittarta.

Dakta Adnan ya ce "Tabbas marasa lafiyan da muke da su musulmai za su dauki tsawon lokaci ana musu sauyin jini na koda."

Ya kara da cewa "Yawancin marasa lafiya musulmai kan mutu yayin da suke jira a yi musu dashen koda saboda rashin samun wanda zai ba su taimakon kodar. Kuma yawansu kullum karuwa yake."

Image caption Yadda kodar dan adam take

'Jira na tsawon lokaci'

A Biritaniya, musulmai wadanda yawancinsu 'yan asalin kudancin nahiyar Asiya ne, su kan yi jiran tsawon shekara guda domin a yi musu dashen koda, fiye da wadanda ba musulmai ba.

Asibitin Sarauniya Elizabeth na kokarin gamsar da musulmai domin su dinga bayar da taimakon koda ga wadanda suke tsananin bukata ko kuma su dinga yadda ana daukar kodar wadanda suka mutu a dasa wa masu bukata da suke raye.

Sai dai wannan al'amari ne mai sarkakayiya, kamar yadda musulmai da yawa ke tababar ko musulunci ya halatta hakan.

'Bambamcin ra'ayi'

Al-kur'ani dai bi yi magana a kan hakan ba kuma Malamai da dama suna da mabambamtan ra'ayoyi a kan hakan.

Dakta Yasser Mustapha wani Malami ne da ke yin wa'azi a masallatai inda yake yin kira ga musulmai da su dinga bayar da taimakon koda, ya ce akwai rikitarwa a al'amarin.

Duk da cewa akwai bambamcin kabila da harshe a tsakanin musulmai, wasu daga Afrika suke, wasu daga Asiya, wasu turawa ne, maganar dai duk daya ce wacce ba wanda zai bugi kirji ya fadi takamaimai amsar.

Tambayar kuwa ita ce Menene matsayar addini a kan bayar da taimakon kuda?

Shin an halatta bayar da taimakon koda a musulunci?

Matsalar rashin bayar da taimakon koda a tsakanin musulmai ba wai a Biritaniya kawai ta tsaya ba.

A watan Afrilu, manyan Malaman musulunci sun taru a jami'ar Karachi da ke Pakistan domin tattauna wannan batu.

Hakkin mallakar hoto AFP

Duk da cewa Malamai da yawa sun nuna goyon bayansu ga wannan batu, wani babban Malami daga majalisar Malamai ta duniya, ya bujiro da batun cewa ko a ranar lahira mutane da aka cire wani bangare na jikinsu za su fuskanci wani kalubale.

Wannan daya ne daga cikin misalan da ba a da tabbas a kansu a cikin akidun musulunci dangane da wannan ra'ayi.

Rehana Sadiq wata ma'aikaciyar asibiti ce kuma mai ilmin addinin musulunci, amma ta ce har yanzu babu wanda ya kira ta daga cikin iyalan majinyantan da suke da su a asibiti suka yi mata maganar za su iya bayar da kodar 'yan uwansu da suke mutu domin a dasa wa wanda ke bukatar dashen koda.