Ghana ta dakatar da gwajin allurar Ebola

Hakkin mallakar hoto AP

Majalisar dokokin kasar Ghana ta ce ba za ta yarda a ci gaba da gwajin allura- riga kafin cutar Ebola a cikin kasar ba sai an samu amincewar masana ilimin kimiyya a ciki da wajen kasar da kuma majalisar dokokin da kanta.

Majalisar dai ta yanke wannan shawara ne bayan da Ministan lafiyar kasar wato Mr. Alex Segbefia ya bayyana a gabanta don yin bayani a kan shirin gudanar da gwajin allurar-riga kafin cutar ta Ebola a kasar.

A makon jiya ne dai majalisar dokokin, tare da Ma'aikatar lafiyar kasar suka dakatar da yunkurin gwajin.

Cutar ta Ebola dai ta hallaka dubban mutane a yammacin Afrika.

A Kasashen Salio, da Guinea, da Liberia ne cutar ta fi illa.

Sai dai yanzu a shawo kan cutar.

Kasar ta Ghana ta kasance cibiyar yaki da cutar a watannin baya