Ramadan: Za a gyara dokar wa'azi a Kano

Image caption Masallaci a Kano

A Najeriya, a yayin da ake shirin fara azumin Ramadana, gwamnatin jihar Kano da ke Najeriya za ta hana wa'azi ba tare da izinin hukuma ba bayan wani malami ya yi batanci ga annabi Muhammad (SAW).

Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya ce an dauki matakin ne ganin yadda ake samun masu da'awar malanta suna wa'azi, amma kuma suke haifar da barna a cikin al'umma.

Alhaji Ganduje ya ce matakin wata hanya ce ta tabbatar da cewa wani mai wa'azi bai sake kwatanta irin kalaman batancin da malamin ya yi ba.

Wasu malamai a jihar sun nuna gamsuwa da matakin.

Ustaz Tijjani Bala Kalarawi ya ce dama a can baya kafin mutum ya fara wa'azi sai ya samu amincewar magabata.

Kudurin dokar dai ya tanadi hukunci ga duk wanda aka samu ya karya dokar.