An jaddada hukuncin kisa kan Morsi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojoji ne suka kawar da gwamnatin Morsi

Wata kotu a Masar ta tabbatar da hukuncin kisa a kan tsohon shugaban kasar, Muhammad Morsi bisa zargin hannu a fasa gidan yari.

Da kuma harin da aka kai wa 'yan sanda, a boren da aka yi a 2011 na hambarar da Hosni Mubarak.

Hukuncin kotun ya biyo bayan tattaunawa da babban Mufti na Masar domin ya fayyace dokar Musulunci a kan hukuncin kotun.

Tun da farko, an yanke wa Mr Morsi hukuncin daurin rai da rai bisa aikin leken asiri.

Haka kuma an yanke wa wasu manyan jami'an kungiyar Muslim Brotherhood hukuncin kisa saboda yi wa kungiyar Hamas ta Falasdinawa da kuma Hezbollah da Lebanon da kuma kasar Iran leken asiri.