Ina son Adam Zango —Nafisa Abdullahi

Image caption Nafisah Abdullahi ta ce tana matukar kaunar Adam A. Zango.

Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisah Abdullahi, ta yi ta-maza, inda ta ce tana matukar kaunar abokin aikinta, jarumi Adam Zango.

Tauraruwar -- wacce ta bayyana matsayinta a shafinta na Instagram -- ta kara da cewa tana fatan Allah zai zaba masu mafi alheri tsakanin ta da shi.

Nafisah, wacce a baya rahotanni suka ambato cewa suna yin soyayya da jarumin amma suka rabu, ta ce ko da yake ta san mutane za su yi mamakin yadda ta fito fili ta bayyana matsayin, amma hakan bai dame ta ba saboda ba za ta iya boye irin kaunar da take yi wa jarumin ba.

A cewarta, "Na san wannan mataki zai sa mutane su rika tambaya ta; ni kai na ban san amsar da zan ba su ba, ban iya boye-boye ba don haka ina son sa (Adam), kuma duk abin da ubangiji ya tsara a tsakaninmu, a shirye nake na dauka".

Nafisah Abdullahi ta bukaci mutane da su yi mata fatan alheri a kan lamarin, ko su yi shiru, kamar yadda wani hadisi ya bayyana.

Wannan dai ba shi ne karon farko da wata jaruma ke nuna kaunarta ga abokin aikinta a masana'antar Kannywood ba.