'Yan Nigeria sun caccaki 'yan majalisa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban majalisar dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki

'Yan Nigeria sun yi amfani da shafukan zumunta na intanet inda suka caccaki 'yan majalisar dokokin kasar a kan batun kudaden alawus da za su karba da suka kai naira biliyan tara.

'Yan majalisar wadanda adadinsu 496, an ba da rahoton cewar za su karbi wadannan kudaden ne a matsayin alawus na sayen tufafin sawa duk da matsalar tattalin arziki da kasar ke ciki.

Jaridar ThisDay ta ba da rahoton cewar kowanne dan majalisar dattijai zai samu naira miliyan 21 da rabi a yayin da kowanne dan majalisar wakilai zai samu naira miliyan 17 da rabi.

'Yan Nigeria cikin fushi sun ce wannan matakin babu adalci kasancewar galibin 'yan majalisar ba za su kare 'yancin talakawa.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Honorabul Yakubu Dogara, shugaban majalisar wakilai

Japeth Omojuwa, ya bayyana wadannan kudaden a matsayin "hauka", inda ya ce sun wuce gona da iri.

Elnathan John kuwa a ra'ayinsa, ya bukaci 'yan majalisar su ji tsoron Allah ka da su karbi kudin saboda a cewarsa "duk wanda ya karba ba zai iya kare kansa a gaban ubangiji ba."

Ita ma Fatima Askira cewa ta yi akwai tsofaffin gwamnoni a cikin 'yan majalisar kuma sun karbi makudan kudade a jihohinsu, ga shi kuma za su karbi wasu kudaden a majalisa.

Dubban mutane ne suka bayyana ra'ayoyinsu a kan wadannan makudan inda wasu ke yin kira a gudanar da zanga-zanga kan wannan batun.

Batun kuma shi ne yake tashe a bakunan 'yan Nigeria da ke amfani da shafukan sada zumunta.