Rasha za ta kara makamai masu linzami

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Wannan batun ya ta ba hankali wasu kasashen duniya

Shugaba Putin na Rasha zai kara sabbin makamai masu linzami fiye da 40 a wani rumbun ajiyar makaman nukiliyar a cikin wannan shekarar.

A cewarsa, makaman za su iya yin babban tasiri kan duk wasu manyan makamai.

Mr Putin ya bayyana hakan ne a wajen bude bikin nuna kayan yaki a Kubinka da ke birnin Moscow.

Ya ce ''A shekarar da muke ciki za mu kara sabbin makamai masu linzami fiye da 40 a rumbun ajiyar makaman nukiliyar mu.

Ba dai a bayyana takamaimai inda za a ajiye makaman ba.

Hakan dai na zuwa ne bayan da Amurka ta bayyana aniyarta na kara yawan dakarunta a gabashin kasashen Turai.