Ni ma ina kaunar Nafisa — Adam Zango

Image caption Falalu Dorayi ya ce Adam A. Zango ya yi farin ciki matuka.

Jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango, ya ce ya yi matukar farin ciki da abokiyar aikinsa, Nafisa Abdullahi ta ce tana matukar kaunarsa.

Jarumin, wanda ya yi magana da BBC ta hannun babban abokinsa, Falalu Dorayi, ya kara da cewa shi ma yana kaunar Nafisa kuma yana fatan Allah ya zaba mafi alheri a tsakanin su.

Ya kara da cewa jarumar ta yi namijin-kokari ganin yadda ta bayyana ra'ayinta a kansa ba tare da shakka ba.

A cewar sa, Nafisa ce mace ta biyu da ta nuna masa soyayya a fili a masana'antar Kannywood.

A karshen makon jiya ne dai jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram cewa tana matukar kaunar Adam A. Zango, tana mai fatan Allah ya zaba masu mafi alheri tsakanin ta da shi.

Nafisah ta ce, "Na san wannan mataki zai sa mutane su rika tambaya ta; ni kai na ban san amsar da zan ba su ba, ban iya boye-boye ba don haka ina son sa (Adam), kuma duk abin da ubangiji ya tsara a tsakaninmu, a shirye nake na dauka."

Nafisah Abdullahi ta bukaci mutane da su yi mata fatan alheri a kan lamarin, ko su yi shiru, kamar yadda wani hadisi ya bayyana.