Wasu 'yan Biritaniya sun yi layar zana

Hakkin mallakar hoto MET POLICE
Image caption Matan Bradford sun bata

'Yan sandan Biritaniya sun yi ammanar cewa daya daga cikin matan nan na Bradford da suka yi layar zana tare da 'yayansu 9, ta shiga cikin Syria.

'Yan sandan yammacin garin Yorkshire da ke Ingila, sun ce sun samu labarin cewar daya daga cikin matan ta gana da 'yan uwanta, wanda hakan ke nuna yuwar tsallakawarsu iyakar zuwa jikin kasar.

Khadija da Sugra da kuma Zohra Dawood, 'yan garin Bradford sun bata ne mako daya da ya wuce tare da yaransu wadanda ke da shekaru tsakanin 3 zuwa 15.

An yi amannar dan uwansu yana yaki tare da mayakan IS a Syria.

Wani babban jami'in 'yan sanda ya ce "Mun samu labarin cewar matan sun gana da 'yan uwansu wadanda suke Ingila wanda haka ke nuna yuwar cewar daya daga cikin matan da suka bata suna kasar Syria."

A ranar Talata mazajen matan guda uku sun yi kira cikin muryar tausayi, inda suke cewa "suna so kuma suna kewar" su inda suka yi kira su dawo gida.

Mutanen sun bata ne tun bayan da suka tafi kasar Saudiyya Umrah.