Musulmai a duniya sun soma Azumi

Image caption A na sa ran musulmai za su yawaita ibada a watan Ramadan

Musulmi a Najeriya sun wayi garin Alhamis da azumi a bakinsu bayan sanarwar da Sarkin musulmin kasar, mai alfarma Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar ya bayar ta ganin jaririn watan azumin Ramadan a daren Laraba.

Ya ce fadarsa ta samu labarin ganin watan ne daga sarakan musulunci a fadin kasar da kuma kwamitin da aka kafa domin ganin watan.

Saboda haka, sarkin musulmin ya ce ranar Alhamis ta zamo daya ga watan Ramadan.

Sultan Abubakar ya kuma kara da jan hankalin al'ummar musulmai da su zage-dantse wajen neman rahamar ubangiji a watan na Ramadan.