Rabin mutane na da kariyar kamuwa da mura

Cutar Mura Hakkin mallakar hoto .
Image caption Cutar Mura

Wani bincike da masana suka yi ya gano cewa, rabi na dukkan mutane na da kariya ta halitta da Allah Ya yi musu daga kamuwa da mura.

Gwajin da aka yi a kan mutane 1,414 ya nuna cewa wannan bangare na garkuwar jikin bil-adama da ake kita T-cells yana kai hari kan yankunan da da kwayoyi iri-iri na mura kan bi su kutsa jikin bil-adama.

Tawagar likitocin daga University College ta London sun ce abu ne mai yiwuwa a iya samar da magani daya tilo na mura da kowa zai iya amfani da shi a duniya.

Sai dai kuma masana kwayoyin cututtuka sun yi kashedin cewa, kwayar cutar mura tana da shu'umanci.

Jikin bil-adama na fitar da wata garkuwa ta kariya daga cututtuka a lokacinda mura ta nemi shiga.

To amma Mura tana iya siffofi ko kamannu ta bijire ma garkuwar jikin bil-adama, wannan shine dalilin da ya sanya ake bukatar wani sabon magani na cutar mura kusan a ko wacce shekara.

T-cells din dai, wani makami ne na musamman a garkuwar jikin bil-adama.

Suna iya zakulo wuraren da cutar mura ta boye.

Wannan na nufin, bayan sun gano wani nau'i na cutar mura , mutane na iya bijere ma sauran nau'oin cututtukan.

Gwajin da aka gudanar a kan mutane 1,500 wadanda ba a yi ma wani riga-kafi ba a cikin tsawon shekaru hudu ya nuna cewar kashi 43 bisa dari suna da kariya ta kamuwa da mura.

Karin bayani