Damisa ta hallaka mutum a Georgia

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Dorinar ruwa

Jami'ai a kasar Georgia sun harbe damisar da ta kashe wani mutum a tsakiyar babban birnin kasar Tibilisi.

Lamarin ya faru ne bayan da daruruwan dabbobi suka tsere daga gidan ajiye namun daji birnin sakamakon mummunar ambaliyar ruwan da ta auku.

Tun da farko, ministan cikin gidan kasar ya ce Zaki ne ya hallaka mutumin, kuma an baza mafarauta dan su farauto shi.

Sai dai daga baya mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida, Nino Giorgobiani ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa damisa ce ta yi kisan ba zaki ba.

Wadanda suka shaida lamarin, sun ce sun ga wata katuwar farar damisa ta nannade mutumin, tare da cafke masa makogwaro.

Kafar yada labaran kasar ta ruwaito cewar damisar ta boye ne a wani gidan ajiye kayayyaki, kana daga bisa ni ta shigo cikin gari dan farautar mai tsautsayi.

Tuni dai gwamnatin kasar ta gargadi mutane da su zauna a gida tun bayan afkuwar lamarin, an dai ga zakuna, da birrai da dorinar ruwa su na ta ninkaya a cikin ruwa a lokacin da tekun Vera ya yi ambaliya sakamakon ruwan da aka sheka kamar da bakin kwarya.

Kusan namun daji 300 ruwan ya tafi da su, wasu kuma suka shiga cikin gari yayin da wasu suka makale a cikin tabo.