Yadda 'yan Nigeria ke fama wajen neman izinin zuwa Biritaniya

A cikin jerin wasikun da muke samu daga 'yan jaridar Afrika da marubuciyar littattafan adabi, Adaobi Tricia Nwaubani, sun yi la'akari da dalilan da ke sa 'yan Najeriya suke jefa rayuwarsu a hatsari wajen kokarin bi ta kowacce hanya domin zuwa Turai a yayin da aka hana su izinin shiga Visa.

Ko da hanyoyin da hukumomi suka amince 'yan Afrika su dinga bin su idan za su ziyarci Turai -- cike suke da tarin matsaloli.

Har yanzu ina iya tuna abin da ya faru a karon farko da na ziyarci ofishin jakadancin Biritaniya a Lagos kusan shekaru goma da suka gabata.

Tun da misalin karfe hudu na asuba masu neman bisa suke fara bin dogon layi a bakin ofishin jakadancin.

Da isa ta wannan waje sai wasu mutane suka tsare ni tare da tambayar takarduna wadanda da su ne zan nemi bisa.

Lokaci zuwa lokaci a kan dan yi hayaniya sakamakon kokarin da sabbin masu zuwa suke yi na wuce wa can gaba a kan layi.

Wani lokaci hakan na afaruwa ne saboda dama can ainahin mai neman bisar ya bai wa zauna gari banzakudi ne domin su bi masa layi don ya huta dogon jira.

"bulala da tsumagiya"

A karshe dai, sai da rana ta take sannan daya daga cikin masu tsaron wajen, wani mai tulelen ciki, ya zo ya bude kofar sashen karbar bisar.

Ya umarce mu mu fara shiga, ya kuma bude katuwar muryarsa yana ihun ce mana "ban da turereniya."

Nan da nan aka fara turereniya, na baya suka dinga tura na gaba; masu karfi suka yi ture marasa karfi.

Ganin yadda mutane ke turereniya ya sa masu tsaron nan suka fara dukan mutane da wata guntuwar bulalarsu ba tare da sun damu ko akwai masu ciki a cikinmu ba ko kuma wadanda suke da rauni.

Nan da nan sai wajen ya rude da hargowa, wasu na ihu wasu na kwakwazo. Amma duk da haka sai muka ci gaba da kokarin kutsawa domin samun shiga wajen da za a yi tantance mu.

Babu wani banbaci cewa ko bisar ziyara ka ke nema zuwa Biritaniya ko ta zama din-din-din. Duk hanya daya ake bi wajen neman bisar.

Image caption Wasu har addu'o'in godiya suke gabatarwa a coci idan suka samu bisa

Amma duk wannan ba komai ba ne idan aka hada da matsalar da ake fuskanta yayin neman bisa a ofishin jakadancin Amurka, wanda ke gaba kadan da inda mu ke, kuma yawan masu neman bisa a wajen ya nunka na ofishin jakadancin Biritaniya sau hudu.

Sai dai da zarar mutane sun samu bisa, to basu da abin farin cikin da ya wuce wannan. Wadanda ba su samu ba kuwa, to tamkar a kansu bakin cikin duniya ya yi aure ya tare.