An sa tukwici don cafke dan Al-Shabab

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya

Rundunar 'yan sandan Kenya ta ce za ta bayar da tukuicin dala 100,000 ga duk wanda ya kama wani Bajamushe, wanda ake zargin cewa yana da hannu a wani hari da kungiyar Al-Shabab ta kai a kasar.

Ana dai zargin cewa Bajamushen mai suna Andreas Martin Muller, yana cikin 'yan bindigar da suka kai samame a wani sansanin sojoji da ke Lamu, ranar Litinin, inda aka kashe masu tayar da kayar baya 11, yayin da sojojin Kenya biyu suka mutu.

Kazalika an kashe wani dan Burtaniya mai suna Thomas Evans, kuma shi ma yana cikin maharan.

Kenya dai na fuskantar hare-hare daga kungiyar AL-Shabab da ke Somaliya.