Sule Lamido ya mika kansa ga EFCC

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'anati EFCC, ta ce ta kama tsohon gwamnan jihar Imo Ikedi Ohakim a gidansa da ke unguwar Asokoro a birnin Abuja.

Mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren ya ce sun kama Mr Ohakim ne, bayan da yaki amsa goron gayyatar da jami'an hukumar suka aika masa.

Haka kuma Mr Uwujaren ya ce tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya kai kansa ofishin hukumar domin ya amsa tambayoyi kan zargin hallata kudin haram da yawansu ya kai biliyoyin nairori.

Hukumar EFCC ta soma gudanar da bincike a kan tsofaffin gwamnonin Nigeria tun bayan da aka mika mulki a watan jiya.

Ana zargin tsofaffin gwamnonin da ake hallata kudaden haramun da kuma waware dukiya al'umma.