An kirkiri sabon maganin Maleriya

Hakkin mallakar hoto WELLCOME TRUST
Image caption Cutar maleriya na hallaka mutane da dama

Masu bincike a jami'ar Dundee sun gano wani sabon sinadari wanda zai iya warkar da cutar zazzabin cizon sauro watau Maleriya.

Maganin kuma zai kare mutane daga kamuwa da ita da kuma kare yaduwarta .

Sashen harharda magunguna na jami'ar da kuma kamfanin yin magungunan maleriya ne suka samar da sinadarin na DDD107498.

Masana kimiyya sun ce sabon maganin zai yi tasiri sosai a kan cutar mai naci fiye da magungunan da ake amfani da su yanzu.

An wallafa cikakken bayanin maganin a mujallar 'Nature'.

Hukumar lafiya ta duniya ta bayar da rahoton cewa an samu bullar cutar maleriya miliyan 200 a shekara ta 2013, kuma cutar ta kashe kimanin mutane 584,000, wadanda mafi yawansu mata ne masu ciki da kuma yara 'yan kasa da shekara biyar.

Ana kara nuna matukar damuwa saboda karfin da maleriya ke karayi inda take bujirewa magunguna, wanda tuni hakan ya bayyana a kan iyakar Miyanmar da Indiya.

'Barazana a zahiri'

Dakta Kevin Read shi ne jagoran binciken ya kuma ce ana bukatar sabbin magunguna da gaggawa.

Hakkin mallakar hoto University of Dundee
Image caption Ana gwajin sabon maganin

Ya ce "bujurewa magungunan da ake amfani da su yanzu da cutar ke yi wata babbar barazana ce a zahiri."

Dakta Read ya kara da cewa "Sinadarin da muka gano yana aiki daban da yadda sauran magungunan maleriya da aka sani suke yi, wanda hakan ke nufin zai yi tasiri sosai wajen kawar da cutar mai naci."

Jami'ar dai ta dade tana aiki da cibiyar samar da magungunan maleriya tun shekarar 2009, domin samar da sabobbin magungunan da za su magance cutar maleriya.

Shugaban cibiyar samar da magungunan maleriyar Dr David Reddy, shi ma cewa ya yi: "Maleriya na ci gaba da yin barazana ga kusan rabin mutanen duniya -- wadanda rabinsu ba su da halin sayen magani."

Hakkin mallakar hoto Dundee University
Image caption A yanzu haka ana yin gwajin sinadarin a cibiyar samar da magungunan maleriya

A yanzu haka ana yin gwajin sinadarin a cibiyar samar da magungunan maleriya, da fatan cewa za a fara gwajin maganin a jikin mutane zuwa badi.