Shugaban Nijar zai ziyarci Japan

Image caption Shugaban Nijar Muhammadou Issoufou

Shugaban kasar Nijar Muhammadou Issoufou ya soma wata ziyarar aiki zuwa Japan domin karfafa dankon zumunci da kasar.

Shugaba Issoufou zai gana da Firayi minista da kuma sarkin kasar ta Japan a ranar Juma'a inda ake tsammanin za su tattauna kan maganar tsaro a yankin Sahel.

Wannan shi ne karo na farko da wani shugaban kasar Nijar ya taba kai ziyara Japan cikin shekaru 29 da suka gabata.

Nijar dai na daga cikin kasashen da ke taka rawa a kawancen sojojin kasashen da ke makwabtaka da tafkin Chadi da ke yakar kungiyar Boko Haram.