Nigeria ta musanta ikirarin Chadi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugabanni kasashen tafkin Chadi sun sha alwashin murkushe Boko Haram

Rundunar sojin Nigeria ta musanta cewa dakarun Chadi sun kaddamar da hare-hare ta sama a kan mayakan Boko Haram a cikin kasar.

Kakakin rundunar, Chris Olukolade ya ce yankin da dakarun Chadi suka yi wa luguden wuta ba a cikin Nigeria yake ba, watakila a yankin jamhuriyar Nijar ne.

Tun da farko, rundunar sojin Chadi ta ce ta kai hare-haren sama kan sansanonin Boko Haram domin daukar fansar harin kunar bakin wake da suka kai a Ndjamena babban birnin kasar.

A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce an lalata sansanonin kungiyar Boko Haram guda shida yayin hare-haren saman, wanda ya jawo asarar rayuka da dama tare da lalata kayayyyaki.

Rundunar sojin Chadi ta ce ta kai hare-haren sama kan sansanonin Boko Haram da ke Najeriya, domin daukar fansar hare-haren kunar bakin wake da ake zargin 'yan kungiyar ne suka kai Njamena, babban birnin kasar.

Hakan na zuwa a yayinda hukomomi a Jamhuriyar Nijar suka ce 'yan kungiyar Boko Haram sun kashe a kalla mutane 38 a lokacin da suka kai hari a kauyuka biyu da ke kudancin kasar.