Wani ya fado daga jirgin sama a London

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wani mutum ya fado daga jirgin sama

Yansanda a Biritaniya na binciken mutuwar wani mutum wanda ake jin ya fado daga karkashin wani jirgin sama.

An gano gawar ne a saman rufin wani shago a yammacin London.

Ana tsammanin mutumin ya boye ne a karkashin kafafun jirgin wani jirgi da ya taso daga Johannesburg zuwa filin jirgin saman Heathrow.

An fahimci cewar an samu mutum na biyu ba cikin hayyacinsa ba a karkashin jirgin a filin jirgin sama.

A cikin watan Satumba 2012, wani mutumin Angola ya mutu bayan da ya fado daga karkashin wani jirgin da ya taso daga Luanda zuwa Heathrow a kan wani titin yammacin London.