Charleston: An kama wanda ya yi kisa a coci

Image caption Dylann Roof, mai shekaru 21

'Yan sanda a Amurka sun samu nasarar cafke matsashin nan mai shekaru 21, Dylann Roof wanda ya shiga coci a garin Charleston na jihar South Carolina ya kuma harbe mutane tara har lahira.

An dai kama Dylann Roof ne a makwabciyar jiharsa ta South Carolinan bayan baza hotunansa da 'yan sandan suka yi a fadin kasar.

Jami'an tsaron sun ce matashin dai sai da ya shiga cocin ya kuma saurari karatun littafin bible na kimanin sa'a guda, kafin daga bisani ya bude wuta akan masu bautar.

An gano Dylann a shafinsa na Facebook yana rataye da tutar kasar Rhodesia da ta kasar Afirka ta kudu ta zamanin wariyar launin fata, wasu alamu da ke nuna fankama irin ta farar fata akan bakake.