Rundunar soji na binciken zargin Amnesty

Image caption Rundunar Sojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kaddamar da bincike kan rahoton da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta fitar da take zargin sojin kasar.

A rahoton, kungiyar Amnesty international ta zargi sojojin Najeriya da tafka ayyukan cin zarafin bil'adama da laifukan yaki a yakin da suke yi da 'yan kungiyar Boko Haram.

A wani taron manema labari da ta kira, rundunar sojin ta ce sam ba ta lamunce wa jami'anta aikata duk wani abu na cin zarafin fararen hulla ko kadan.

Ta yi kira ga kungiyar da sauran 'yan kasar da su ba ta lokaci domin yin binciken cikin tsanaki.

Amnesty ta yi zargin cewar an kashe mutane kusan 8,000 a karkashin kulawar sojin Nigeria a cikin yaki da Boko Haram.