Matatun man fetir za su koma aiki a Najeriya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Matatun man Nigeria sun dade ba sa aiki

Matatun man fetur na Nigeria guda hudu za su koma aiki gadan-gadan a cikin watan Yuli mai zuwa.

Kakakin kamfanin man fetur na kasar, Ohi Alegbe ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar matatun mai biyu da ke Fatakwal ne za su soma aiki, sannan bayan an kamalla gyara sai na Warri da kuma na Kaduna su soma aiki.

Reuters ta ambato Kakakin na cewar idan matatun man suka soma aiki za su tace danyen mai lita miliyan 19 watau kusan rabin adadin danyen man da ake bukata a kasar.

Ana amfani da man fetur lita miliyan 40 a kowace rana a Nigeria, kenan ko da matatun mai na aiki, za a samu gibin lita miliyan 21 da za a shigo da shi daga kasar waje.

Nigeria ce kasar da ta fi kowacce samar da danyen mai a Afrika amma kuma ana yawan fama da karancin man fetur a kasar saboda matsalar matatun man kasar da ba sa aiki yanda ya kamata.