An kai ma 'yan sanda hari a Burundi

A Burundi an kai wasu jerin hare-hare da gurneti akan 'yan sanda a Bujumbura, babban birnin kasar.

Jami'an tsaro sun ce harin, wanda aka kai cikin dare, ya jikkita akalla 'yan sanda tara.

Hare-haren gurnetin sun auku ne a lardunan da a kwanakin baya aka yi mummunan zanga-zangar adawa da yunkurin tazarce na Shugaba Pierre Nkurunziza karo na uku a karagar mulki.

'Yan sanda sun dora laifin akan 'yan adawa.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ce akalla mutane 70 suka rasu wasu 500 kuma suka sami raunuka tun bayan da aka fara zanga-zanga a watan Aprilu.

Karin bayani