An tsare dan-jaridar Al-Jazeera a Jamus

Hakkin mallakar hoto Reuters

Gidan Talabijin na Al Jazeera ya yi kira da a saki daya daga cikin manyan ma'aikatansa Ahmed mansour nan take, wanda aka tsare a Jamus bisa wata bukata ta kasar Masar

Wani babban jami'in gidan Talabijin din na Al Jazeera , yace bai kamata sauran kasashe su rika bari ana amfani da su wajen musgunawa 'yan jarida ba

A wani rubutu da yayi a shafinsa na Facebook, Mr Mansour wanda aka tsare, ya ce ya nunawa hukumomin Jamus din wani sakon email daga 'yan sandan kasa da kasa na Interpol, dake cewa su fa ba sa nemansa.

A bara ne dai wata Kotu a birnin Alkahiran kasar Masar din ta yankewa Mr. Mansour din hukuncin daurin shekaru 15 a gidan Yari, akan zarge zargen azabtarwa, ba tare da ya halarci zaman kotun ba

Al -Jazeeran dai ta bayyana zarge- zargen da cewa ba gaskiya bane