An shawarci Buhari ya cire tallafin mai

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

An shawarci sabon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya soke tsarin bayar da tallafin mai a kasar.

Haka kuma an nemi ya sayar da matatun mai hudu na kasar ga 'yan kasuwa masu zaman kansu.

Kwamitin mika mulki wanda ya kunshi jami'ai daga jam'iyyar APC ta Buharin ne bada shawarwarin a rahoton da ya mika mashi.

Kwamitin ya kuma bada shawarar kafa sabbin kananan matatun mai.

Lamarin tallafin man yana da tsada sannan ana kuma danganta shi da badakalar cin hanci.

A baya dai yunkurin rage tallafin man ya haifar da jerin zanga-zanga a kasar.

Karin bayani