'Yan sanda za su toshe kafofin daukar 'yan jihadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan Jihadi na IS na rike da yankuna a Syria da Iraqi

An kirkiro da wani sashe na 'yan sandan nahiyar Turai, domin gane mutanen da suke amfani da kafofin yada labarai na sada zumunta ,wajen daukar matasa musulmi domin yiwa mayakan IS Yaki

Hukumar 'yan sandan nahiyar Turai Europol, tace ana aikewa da sakonnin twitter 100, 000 a kowacce rana, daga wadanda keda alaka da kungiyar dake ikirarin yin jihadin, wacce kuma ke iko da wasu yankuna a kasashen Syria da kuma Iraqi

Ta ce sabon sashen na 'yan sanda, zai yi yunkurin lalata irin wadannan kafofi na mayakan jihadin cikin sa'oi biyu da gano su.

Sabon sashen 'yan sandan, zai soma aiki ne, ranar daya ga watan Yuli.