Marasa galihu na zanga-zanga a Ghana

Image caption 'Yan zanga-zanga a Ghana

'Yan sanda a Accra na kasar Ghana sun fesa barkonon-tsohuwa a kan dubban mutanen da ke yin zanga-zanga saboda za a rushe unguwar matalauta mafi girma a birnin.

Masu zanga-zangar sun yi ta kona tayoyi, sannan suka rika jifa da duwatsu da kuma tare hanyoyi.

Unguwar matalautan -- mai suna Sodom da Gomorrah -- ita ce unguwar da ta fi tsufa a kasar, kuma fiye da mutane 50,000 ke zaune a cikinta.

Hukumomi a kasar sun ce unguwar tana hana ruwa ya rike wucewa zuwa teku, kuma hakan ne ya jawo ambaliyar ruwan da aka yi a birnin a farkon watan nan, wacce ta yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane 150.