An kammala taro a kan basussukan Girka

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Firayiministan Girka Alexis Tsipras

Shugabannin kasashen Tarayyar Turai sun kammala wani taron gaggawa a Brussels, suna masu taka tsan tsan da yakinin da suke da shi na cimma yarjejeniya da zata kare kasar Girka kasa biyan basussukan da ake binta.

Gwamnatin Girka ta ce zata samar da kudi Yuro biliyan takwas ta hanyar kara kudin haraji da kara daukan matakan tsuke bakin aljihu domin ta sanyaya ran wadanda suka bata rance.

An kira taron ne domin duba sabbin matakan da Girkan ta gabatar musu zata dauka, a yayin da wa'adin 30 ga watan Yunin nan, na ta biya Asusun bada lamuni na duniya basussukan da ya bata ke kawo jiki.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce akwai ci gaba a sabbin matakan da Girkan ke shirin dauka, sai dai duk da haka akwai sauran aiki a gaba.

Shugaban Tarayyar Turai Donald Tusk ya ce ministocin kudi na kasashen kungiyar zasu sake taro ranar gobe Laraba a kokarin cimma yarjejeniya ta karshe dangane da warware sarkakiyar basussukan na kasar ta Girka.