An kama babban jami'in leken asirin Rwanda

Image caption Karenzi Karake

Babban jami'in leken asiri na kasar Rwanda -- wanda ake nema ruwa a jallo a kasar Spain saboda zargin aikata laifukan yaki -- ya shiga hannun jam'ian tsaro a London.

Tashar watsa labarai ta BBC ta gano cewa 'yan sandan Biritaniya sun kama Karenzi Karake a filin jirgin sama na Heathrow a ranar Asabar.

Hukumomin 'yan sandan sun tabbatar da cewa Karake mai shekaru 54 ya bayyana a gaban kotun Majisre ta Westminster bayan an tsare shi bisa umurnin kama shi a kasashen Turai.

Karake shi ne babban Daraktan hukumar leken asiri ta kasar Rwanda, kuma ya fafata a yakin basasan kasar daga 1990 zuwa 1994.

Yana daga cikin kwamandojin Rwanda 40 da wani alkali a kasar Spain ya samu da laifi a shekarar 2008.

Kotun kasar Spain din ta ce lokacin Karake yana shugaban sashin leken asiri na sojin Rwanda, ya bayar da umurni an yi kisan kare dangi da yawa.

An kuma zarge shi da bayar da umurnin kashe wasu 'yan kasar Spain 3 da ke aiki kungiyar likitoci ta Medicos del Mundo.