Babu komai a asusun gwamnati — Buhari

Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ba ta gaji kudade masu yawa ba a asusun Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce gwamnatinsa ba ta samu kudade masu yawa ba a asusun Najeriya da ta gada daga gwamnatin Shugaba Jonathan.

Buhari ya yi wannan jawabi ne a Abuja, kasa da sa'o'i 24 kafin ganawar sa da gwamnonin jihohin Najeriya.

Shugaba Buhari ya ce abin takaici ne yadda Shugaba Jonathan ya bari aka kwashe kudaden da ke asusun gwamnatin kasar, yana mai cewa hakan ya sa Najeriya ta fada mawuyacin hali.

Ya bukaci 'yan jaridar da ya gana da su da su taimaka masa wajen yi wa 'yan kasa bayanin irin mawuyacin halin da ya tsinci kasar a ciki, domin su yi hakuri da tsare-tsaren da zai yi wajen inganta rayuwarsu.

Shugaba Buhari ya ce ya gaji bashin miliyoyin dala, inda ta kai ba a iya biyan albashin ma'aikatan gwamnatin tarayya da na jihohi.

Shugaba Buhari na ganawa da gwamnonin ne domin samar da hanyar fitar da kasar daga cikin mummunan halin da ta fada a ciki, musamman yassa za a biya albashin ma'aikata da aka kwashe wata da watanni ba a biya su ba.