Buhari zai je Kamaru bayan Ramadan

Image caption Shugaban kasar Kamaru Paul Biya, ya gayyaci Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zuwa kasar sa domin su tattauna hadin gwiwar yaki da ta'addanci.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na'am da gayyatar shugaban kasar Kamaru, Paul Biya ya yi masa domin ya kai ziyara kasar.

Manufar ziyarar ita ce tattauna batun yadda za a kawar da kungiyar Boko Haram wacce ta hallaka dubban mutane a kasashen biyu

Minista a gwamnatin Kamaru, Mr. Sadi Rene Emmanuel ne ya mika wa Buhari wasikar gayyatar daga wajen Shugaba Biya.

Shugaba Buhari ya ce zai ziyarci Kamarun bayan an kammala azumin Ramadan, inda ya kuma jaddada cewa zai yi amfani da iliminsa na aikin soja da kuma tallafi daga kasashen waje, domin kawo karshen matsalar ta'addanci.

Ya kuma kara da cewa "Na yi farin ciki da Shugaba Paul Biya ya gayyace ni, na ziyarci Chadi da Nijar a kan wannan lamari, kuma na yi niyyar zuwa Kamaru amma sai na samu gayyatar ziyartar taron G7 a Jamus".

Shugaba Buhari ya yi yaba kokarin da kasashen da ke makwabtaka da Najeriya, har ma da Kamaru a yaki da Boko Haram, ya kuma yi kira da a kara zage damtse.

Ministan ya tabbatar wa Shugaba Buhari, cewa Shugaba Biya ya sha alwashin yaki da kungiyar Boko Haram kuma a shirye ya ke da a hada gwiwa domin a samun nasara.