Bam ya kashe mutane 10 a Gujba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram ta kona gidaje da dama a hare-harensu

Wata 'yar kunar-bakin-wake ta hallaka mutane kusan 10 tare da raunata wasu da dama a kasuwar Gujba da ke jihar Yobe.

Lamarin ya auku ne da safe lokacin da mutane ke hada-hada a cikin kasuwar.

Harin na zuwa ne kwana guda bayan da wasu mata 'yan kunar-baki-wake suka tayar da wani bam a kasuwar tashar Baga da ke Maiduguri inda mutane fiye da 20 suka rasu.

Kungiyar Boko Haram wadda ta addabi yankin arewa-maso-gabashin kasar, ta hallaka dubban mutane tare da raba wasu fiye da miliyan daya da muhallansu.

A yanzu Nigeria ta daura dammarar yaki da Boko Haram inda ta hada-gwiwa tare da kasashen Nijar da Kamaru da kuma Chadi domin kawar da kungiyar.