An ceto kananan yara 48 a Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Ana tilasta wa kananan yara aiki a gonakin Koko a Ivory Coast

Wani aikin hadin-gwiwa a kudu maso yammacin kasar Ivory Coast inda ake noman koko, ya yi sanadiyyar 'yantar da yara kananan 48 da kuma tsare masu fataucin yaran su 22.

'Yan sandan kasa da kasa na Interpol sun ce yaran wadanda keda shekarun da suka kama daga biyar zuwa 16 da haihuwa, sun fito ne daga kasashen Burkina Faso da Gini da Mali, da ma bangaren arewacin kasar ta Ivory Coast.

Suka ce wasu daga cikin yaran suna aiki ne a gonaki a matsayin bayi karkashin tsauraran yanayi, ba tare da ana biyansu albashi ba ko kuma ma tura su makaranta.

'Yan sandan kasar Ivory Coast 200 ne suka shiga cikin wannan aiki na ceto, tare da hadin-gwiwar 'yan sandan kasa da kasa na Interpol, da kuma hukumar kula da ci-rani ta kasashen duniya.