Boko Haram ta kai hari Bosso

Hakkin mallakar hoto BOKO HARAM
Image caption Rahotanni na cewa wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari kauyaen Yebbi, a Bosso, jamhuriyar Nijar.

Rahotanni daga jamhuriyyar Nijar na cewa wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai hari kauyen Yebbi, a yankin Bosso a ranar Talata da daddare.

Mazauna garin wadanda mafi yawansu masunta ne sun ce an rasa rayuka sakamakon hari.

Yawancin wadanda abin ya shafa 'yan gudun hijira ne da suka gudu daga Najeriya zuwa Nijar din sakamakon hare-haren da ake kai wa kauyukansu.

Kungiyar Boko Haram dai sun tsaurara kai hare-hare a Najeriya da Njiar a makwannin da suka gabata.