Babban ma'aikaci a Google ya mutu

Google Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Google

Google ya tabbatar da rasuwar wani shugaban kamfanin sakamakon hadari da ya rutsa dashi a Cannes da ke Faransa.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce mamacin yana daya daga cikin mambobin Google masu hazaka.

Hadarin ya rutsa da shi ne bayan da wata motar tasi ta kade shi, a lokacin da yake kan hanyar sa ta zuwa halartar wani bikin wasan zakuna.

Wannan bikin dai ya kasance wani wajen baje kolin hajar kayayyakin kamfanonin a kowace shekara.

"Muna jajantawa iyalai da abokan arzikin mamacin" inji Kamfanin na Google.

Jami'an 'yan sanda sun shaidawa manema labarai cewa mutumin mai shekaru 30 a duniya Ya mutu ne a ranar 21 ga watan da muke ciki.

Wannan dai shi ne karo na biyu da kamfanin ya yi rashin ma'aikacinsa a 'yan watannin nan.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan shi ne karo na biyu da Google ya rasa ma'aikatansa

A watan Aprilun da ya gabata ma daya daga cikin shugabannin kamfanin, Dan Fredinburg ya mutu sakamakon girgizar kasar da ta ritsa da shi a kasar Nepal.