Budurwar da ta yi tayin mota na asibiti a Kano

Hakkin mallakar hoto Freedom radio
Image caption Hukumomin lafiya sun ce Zainab Abdulmalik tana fama da tabin hankali.

A Najeriya, hukomomin lafiya a jihar Kano sun ce matashiyar nan da a makon jiya ta je wani gidan rediyo domin neman mijin aure, yanzu haka tana jinya a asibitin masu tabin hankali.

Hukumomin sun ce Zainab Abdulmalik, mai shekaru 22 a duniya, dama can tana karbar magani a kai-a kai, amma daga baya-bayan nan ciwon na ta ya ta'azzara.

Matashiyar dai ta ja hankalin jama'a ne lokacin da ta je gidan rediyon Freedom da ke jihar ta Kano, inda a wani shiri, ta yi alkawarin sayen mota da gida ga duk mutumin da zai aure ta, tana mai cewa ta yi hakan ne bayan wani saurayinta ya yaudare ta.

Lamarin dai ya dauki hankalin daruruwan mutane, wadanda suka je gidan rediyon domin ta zabi guda daga cikin su, kuma aka yi sa'a ta zabi wani.