Ebola: Masu fama da zazzabi ba sa samun magani

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cutar Ebola a Guinea ta sa masu fama da zazzabi tsoron zuwa asibiti

Masu bincike sun ce fiye da masu fama da zazzabin cizon sauro dubu 70 ne ba su je an duba su a kasar Guinea a bara ba, saboda barkewar cutar Ebola.

Wani bincike wanda masana kimiyya a Amurka suka jagoranta, ya yi nuni da cewa cutar malariyan da akai ta samu ka iya zama dalilin karuwar mace- macen da aka samu cikin kasar, fiye da cutar ebolar ita kanta

Rahotan ya ce masu fama da cutar Malariyar ba su sami magani ba, ko dai saboda dakunan shan magungunan sun kasance a rufe, ko kuma saboda marasa lafiya na tsoron neman taimako