Zafi na ci gaba da hallaka 'yan Pakistan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Galibin wadanda suka mutu tsofaffi ne

Gwamnatin lardin Sindh a Pakistan ta ba da hutu a Karachi inda yanayi mai tsananin zafi ya hallaka sama da mutum dari takwas.

Ana fama da wannan yanayi na zafi ne a daidai lokacin da ake al'umar Musulmi ke azumin watan Ramadana.

Malamai dai sun ba da fatawar cewa masu aikin karfi a wannan yanayin za su iya shan azumin.

Karin mutanen dai sun mutu ne sakamakon galabaitar da suka yi a asibitocin dake birnin Karachi.

Likitocin sun ce sun shiga damuwa kan yadda matsalar ta kara ta'azzarara a rana ta biyar.

'Rashin Lantarki'

Hasarar rayukan ta kara tsananta ne saboda tsawon lokacin da aka dauka babu wutar lantarki ga kuma matsanancin karancin ruwan sha.

Akasarin wadanda abin ya fi shafa tsofaffin ne daga iyalai marasa galihu.

Mahukuntan lardin Sindh da kuma gwmnatin tarayya a Islamabad na zargin junasu kan abkuwar bala'in.

Jama'a da dama na nuna fushinsu a fadin kasar kan abinda suka ce gazawar mahukuntan wajen tashi tsaye su kare rayukan jama'a.