Leken Asiri: Hollande zai gana da Obama

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana zargin Amurka da cin amanar abota

Shugaban Faransa, Francois Hollande zai tattauna da shugaba Barack Obama a kan wani bayanin da aka kwarmata cewa jami'an Amurka sun leki asirin shugaba Hollande da wasu shugabannin Faransa biyu da suka gabace shi.

Shafin na Wikileaks, ya bayyana cewar hukumar leken asirin Amurka, ta yi leken asiri akan Mr Hollande da Nicolas Sarkozy da kuma Jacques Chirac a tsakanin shekara ta 2006 zuwa shekara ta 2012.

Tuni gwamnatin Faransar ta aikawa da Jakadan Amurka a birnin Paris sammace bisa ikrarin da shafin nan na kwarmata bayanai

Mr Hollande ya kira wani taron gaggawa a kan wannan al'amari, ya na mai cewar ko kadan kasar Faransa ba za ta amince da duk wani mataki da ke barazana ga tsaron kasar ta ba.

Sai dai gwamnatin Amurka ta ce ba za ta ce uffan ba a kan zargin wani mataki takamaimai na leken asiri ba.

Dama dai a can baya an taba zargin hukumar leken asirin ta Amurka da satar sauraren maganganun shugabar gwamnatin kasar Jamus, Angela Merkel da kuma shugabannin kasashen Brazil da Mexico.