Burundi ba zata halarci tattaunawar Majalisar dinkin duniya ba

Burundi Protesters Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Burundi Protesters

Gwamnatin Burundi tace ba zata bi sahun tattaunawar da majalisar dinkin duniya ta shirya gudanarwa ba domin warware zaman dar-dar din da ake gabanin babban zaben kasar mai cike da rudani.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Edouard Nduwimana ya ce ba za canja jadawalin zaben ba.

An dai shafe lokaci mai tsawo ana gudanar da zanga-zangar kin amincewa da tazarcen shugaba Nkurunziza a karo na uku.

Manyan kusoshin siyasar kasar biyu sun arce zuwa Belgium. Za dai a gudanar da zaben shugaban kasar ne a cikin wata mai zuwa, yayinda za a gudanar da na 'yan majalisar dokokin kasar kuma a ranar litinin mai zuwa.