Mataimakin shugaban Burundi ya arce

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gervais Rufyikiri ya ce ana barazana ga rayuwarsa

Daya daga cikin mataimakan shugaban Burundi, ya arce zuwa kasar Belgium, yana cewa ana yin barazana ga rayuwarsa.

Garvais Rufyikiri ya yi suka ga yunkurin Shugaba Pierre Nkurunziza na neman tazarce.

Mr Rufyikiri ya yi kira ga Shugaban na Burundi, da ya sanya bukatun 'yan kasar Burundi gaba da na shi bukatun na kashin kansa.

"Har zuwa wannan lokacin, ba a kore ni ba ko kuma dakatar da ni daga cikin Jam'iyyar CNDD-FDD, don haka ina ciki a matsayin cikakken wakili, tare da sauran 'yan jam'iyyar, wadanda suma suke hamayya da takarar Nkurunziza ta neman shugabanci a karo na uku," in ji Rufyikiri.

Ana dai ta zaman dardar a kasar, inda har mutane da dama suka nemi mafaka a harabar ofishin jakadancin Amurka a Bujumbura.